YAU NE RANAR DA AKA WARE DAN GUDANAR DA GANGAMIN RUSHE SARS



A yau ne, gamayyar kungiyoyin kare hakkin dan Adam suka tsara gudanar da zanga zangar lumana a manyan biranen kasar nan don tursasawa Sufeto Janar na ‘yan sanda kan ya rusa rundunar nan ta yaki da miyagun laifuka wadda aka fi sani da SARS.

An dai tsara gudanar da zanga zangar ce a biranen Abuja, Legas, Kaduna, Port Harcourt, Akwa, Ibadan, Warri, Jos. Kungiyoyin dai sun nuna cewa daukar matakin ya zama dole ganin yadda rundunar ta kamo ta cin zarafin al’ummar da ba ruwansu a maimakon kare dukiyoyi da rayuka.

Sai dai kuma, rundunar ‘yan sanda ta fito fili ta nuna cewa idan har aka rusa rundunar, ‘yan Fashi da makami, masu satar mutane da dabbobi za su rika cin karensu ba babbaka inda ta nuna cewa an kafa rundunar ce don kawar da wadannan miyagun. Kakakin Rundunar, ‘Yan sanda , Jimoh Moshood ya ce, masu aikata miyagun laifuka na da hannu wajen shirya zanga zangar.

You may also like