A Yau Ne Za A Gudanar Da Zaben Shugaban Kasar Amurka


 

A yau ne mutanen kasar Amurka za su gudanar da zaben shugaban kasa karo na 45 a kasar, wanda zai maye gurbin Barack Obama.

Rahotanni daga birnin Philadelphia na jahar Pennsylvania a kasar Amurka na cewa, a daren jiya ‘yar takarar shugabancin kasar karkashin inuwar jam’iyyar Democrat Hillary Clinton, tare da mai gidanta Bill Clinton, gami da shugaban kasar ta Amurka Barack Obama, sun taru a wani dandali da ke birnin na Philadelphia, tare da magoya bayan jam’iyyar Democrat fiye da dubu 40, inda suke yakin neman zabe na karshe.

Shi ma a nasa bangaren dan takarar shugabancin kasar ta Amurka karkashin inuwar jam’iyyar Republican Donal Trump, ya halarci tarukan da aka shirya masa a jahohi 5 a jiya Litinin, kuma zai kammala da jahar ta Pennsylvania.

Wannan dai shi ne zaben shugaban kasa da za a gudanar da yake cike da tone-tone da kuma kalaman batanci a tsakanin ‘yan takarar shugabancin kasar, musamamn ma na manyan jam’iyyun siyasar kasar guda biyu, Republican da kuma Democrat.

Jin ra’ayin jama’a kan zaben ya nuna cewa Hillary Clinton tana a gaban Donald Trump da tazara ta digo 4, duk kuwa da cewa da dama daga cikin Amurka sun nuna rashin gamsuwarsu a kan dukkanin ‘yan takarar biyu.

You may also like