Yau, Ranar Malamai Ta Duniya, An Bayyana Muhimmancinsu Ga Cigaban Dan Adam



PLATEAU, NIGERIA – Majalisar dinkin duniya ta kebe ranar biyar ga watan Oktoban kowace shekara a matsayin Ranar Malamai ta Duniya. Makasudin kebe ranar shi ne a yaba da aikin da malamai ke yi a kuma nemi hanyoyin magance matsalolinsu.

Yau Bikin Ranar Malamai Ta Duniya An Bayyana Muhimmancinsu Ga Rayuwa

Yau Bikin Ranar Malamai Ta Duniya An Bayyana Muhimmancinsu Ga Rayuwa

Malam Isiyaka Abdullahi da ke garin Doma a Jihar Nasarawa, ya ce akwai karancin kayan aiki da rashin isassun malamai. Haka kuma Komared Joshua Bala Bwede ya ce rashin biyan albashin malamai ya na dukufar da kuzarinsu na aiki.

Watanni takwas kenan tun bayan da malaman jami’o’i a Najeriya su ka shiga yajin aiki, har yanzu sun kasa daidaitawa da gwamnatin tarayya.

Dakta Peter Michael da ke jami’ar Modibbo Adama a Jihar Adamawa, ya ce tilas ne malamai su shiga yajin aiki don ayi gyara., amma a kullum gwamnati na cewa tana iyakar kokarinta.

Yau Bikin Ranar Malamai Ta Duniya An Bayyana Muhimmancinsu Ga Rayuwa

Yau Bikin Ranar Malamai Ta Duniya An Bayyana Muhimmancinsu Ga Rayuwa

Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong ya ce ya zamo dole a sami ilimi mai inganci ta hanyar samar da kwararrun malamai.

Ko a bara sai da shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya amince da bai wa dalibai dake da niyyar zama malaman makaranta, tallafi na Naira dubu saba’in da biyar, yayin da wadanda ke kwalejojin Ilimi za su samu tallafin Naira dubu hamasin don ba su kwarin gwiwar samar da ilimi mai inganci.

Saurari cikakken rahoton daga Zainab Babaji:

You may also like