Yau shekaru 20 da ‘yan Taliban suka yi nasarar kwace birnin Kabul fadar gwamnatin Afghanistan, in da suka ci gaba da mulki har zuwa shekara ta 2001, lokacin da rundunar kawance karkashin jagorancin Amurka ta kwace shi daga hannunsu.
Rufe gidaejn sinima da wuraren cin abinci da kuma hana wa maza aske gemu, wadannan na daga cikin dokoki na farko da ‘yan kungiyar Taliban suka kafa a birnin Kabul da kuma sauran sassa na kasar ta Afghanistan.
‘Yan Taliban wadanda ke ikirarin kafa shari’ar musulunci a kasar, sun rika zartas da hukunce-hukunce da suka hada da kisa ko kuma yanke gabobi akan wadanda aka sama da laifin karya dokokin da suka kafa.
To sai dai sakamakon alakar da ke tsakanin kungiyar ta Taliban da kuma al-Qaeda da kuma harin da aka kai wa Amurka a ranar 11 ga watan Satumbar shekara ta 2001, hakan ya sa Amurka da kuma kawayenta suka kaddamar da farmaki tare da kawo harshen mulkin kungiyar.
To sai dai har zuwa yau, kungiyar ta Taliban na ci gaba da kasancewa babbar barazana ga sha’anin tsaron kasashen Afghanistan da Pakistan da kuma ita kanta Amurka.