Yaune Ranar Da Kungiyoyi Daban-daban Za Su gudanar Da Zanga Zangar Nuna Rashin Bukatar Majalissa A Nigeriya


Kungiyar ISMOG ita ma tana daga cikin kungiyoyin da za su gabatar da zanga -zanga a Majalisar wakilan Nijeriya da ta dattawa a yau Talata sha biyar ga wannan wata.
Wannan zanga-zanga za’a yi ta ne domin neman ‘yancinmu dangane  da badakalar dake faruwa a Majalisa da kuma nunawa duniya ra’ayinmu na rashin bukatar Majalisa a Nijeriya.
Ra’ayin masu zanga-zangar shine ita ma Nijeriya ta shiga sahun kasashen da babu wata Majalisa wakilai ko ta dattijan. Wanda ta haka ne za a samu cigaba mai amfani duba da yadda ‘yan Majalisar suka daukaka bukatunsu fiye da na al’ummarsu. 

Ya kai Dan uwa ‘yar  kufito mu yi yaki da cin hanci da rashawa da ya yi katutu a zukatun ‘yan Nijeriya. Ku sani wannan zanga zanga ta lumana ce kuma tana da sharudam
Za’a hadu filin  hadin  kan ‘yan kasa kusa da Millenium Park, bayan Hilton Hotel. Kafin daga bisani a dunguma zuwa Majalisar tarayya domin gabatar da zanga zangar.
Domin karin bayani za ku iya tuntubar wannan lambar 08032682944
Sanarwa ga wadanda suke garuruwan kusa da Nyanya. Za ku iya zuwa Mararraba daidai wajen juyawar mota dake kusa da Access banka  da Cocin ECWA, akwai motar zuwa kyauta. Za a fita karfe takwas na safe 08:00am.
Domin karin bayani za ku iya tuntubar wannan lamba 08135583932.

Sama da mutum dubu biyu ne ake  sa ran za su halarci zanga-zangar.

You may also like