A yau ne, ake sa ran Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki zai karanta wasikar Shugaba Muhammad Buhari na sake gabatar da Ibrahim Magu don majalisar ta tantance shi a matsayin Shugaban Hukumar EFCC.
Idan ba a manta ba, a watan da ya gabata ne, majalisar ta ki amincewa da tantance Magu sakamakon wani rahoton hukumar DSS wanda ya zarge shi da wasu laifuka wanda hakan ya sa Shugaba Buhari ya umarci Ministan Tsaro kan ya gudanar da bincike kan rahoton.