Yawan Musulmi Na Dada Yawa A Kasar Madagaska A Ciki Yan Shekarun Da Suka Gabata


Jawamn al-ummar Musulmi a kasar Madagaska ya karu a cikin shekaru bakwai da suka gabata daga kashe 1.1% zuwa kashi 15% .

Kamfanin dillancin labarai na IKNA ya bayyana cewa bisa kididdigan da aka bayyana a baya bayan nan na yawan mutane da kuma addinansu a kasar Madagaska ya nuna cewa yawan masu shiga addinin musulunci ya karo so sai.

Dangane da dalalin karuwar musulmi a kasar ta Madagaska Jeen Jark Ruwano wani masanin harkokin musulmi a kasar ya bayyanawa IKNA kan cewa dalila da suka sanya mutanen kasar Madagsaka suke rungumar addinin musulunci sun hada da tsarin rayuwan daddaiku da kuma na zamantakewa wanda addinin musulunci ya kebantu da su.

Daga kasrhe Jark ya kara a cewa ayyukan ta’addanci wanda ake dangantakwa ga wasu musulmai bai da tasiri a karuwar yawan musulmi a kasar ta Madagaska.

You may also like