Yawan Sauyawa Alkalai Wuraren Aiki Na Daga Cikin Kalubalen Ma’aikatar Shari’a- EFCC
Cikin wata kasida a yayin wani taro a Kano, shugabar sashin kula da lamuran shari’u ta ofishin shiyyar Kano na hukumar ta EFCC Barrister A’isha Tahar, tace amfani da ‘yan kasuwa a kokarin badda sawun kudaden da aka sata daga lalitar gwamnati na daukar lokutan Jami’an hukumar wajen gudanar da bincike. Tace su-ma lauyoyin dake kariya ga wadanda ake tuhuma na taka rawa wajen tsawaita shari’un dake gaban kotu, ta hanyar fakewa da wasu sidirori na kundin doka, domin kawai su kawar da hankalin Jama’a daga jigon bantun da ake kara akan sa.

Shugaban hukumar EFCC Abdulrashid Bawa wanda kwamandan hukumar mai kula da shiyyar Kano Faruk Dogon Daji ya wakilta, yace hukumar ta samu nasara kan kararraki fiye da dubu uku daga watan Janairu zuwa watan jiya na Nuwamba a sassan Najeriya, ciki kuwa har da 240 da aka samu a shiyyar Kano.

A cewar sa, sabanin yadda mutane ke tunani, hukumar bata samun katsalandan daga gwamnati ko jami’anta, kuma hakan na daga sirrin nasarorin da take samu a yanzu. Yana mai bada misali da yadda hukumar ta kama tare da gurfanar da wasu daga cikin Jami’an gwamnati a gaban kotu, tsohon babban akanta na kasa da wasu jami’ai na gwamnati, bisa tuhumar da badda sawun kudaden jama’a.

Yayin da shugabancin hukumar EFCC ke cewa, baya samun katsalandan daga gwamnati, masana dokoki da shari’a sunce lauyoyin dake aiki a hukumar na fuskantar kalubale wajen kiyaye ka’idoji da tanade-tanaden aikin lauya, al’amarin da ka iya zama wani nau’in katsalandan ga tsarin ayyukan hukumar.

Farfesa Nasiru Adamu Aliyu mai lambar aikin Lauya ta SAN, wanda ke koyar da aikin lauya a Jami’ar Bayero Kano, yace su lauyoyin da suke aiki a hukumar sun sani cewa, a wasu lokutan shugabanni a hukumar ba sa sakar musu mara suyi aiki yadda ya kamata dai-dai da ka’idar aikin lauya. Yace batutuwa na mu’amalar kudi tsakanin mutum-da-mutum ba su cancanci hukumar ta mika su gaban kotu ba.

Hakan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da Najeriya ke kokarin nunawa duniya matakan dakile ayyukan rashawa da hukumomin kasar ke dauka na haifar da sakamako mai kyau.

Saurafri rahoton cikin sauti:Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like