
Tsohon shugaban jam’iyar APC na Kasa, Cif Bisi Akande,yayi gargadin cewa yawan amfani da kudi makudai da akeyi a harkar siyasa, nan ba dadewa ba zai kashe tsarin siyasar Najeriya idan har ba’ayi maganin haka ba.
A wata sanarwa da ofishin yada labaransa yafitar, an rawaito tsohon gwamnan na Jihar Osun na cewa ” siyasar kudi na rage darajar ginshikin dake sawa a shiga siyasa wanda shine don a bautawa jama’a. Yan Siyasar Najeriya tamkar suna zaune ne akan nakiya dake jiran fashewa kan yadda yawan amfani da kudi a siyasa ke karuwa.
” Irin wannan siyasa bakuwa ce a wurin mu,tuni ta fara kore dalilin dake sawa mutane su shiga siyasa, yakamata ayi maganin haka domin barazana ce ga tsarin dimakwaradiya.”yace.