Ya’yan jam’iyar PDP sun fice daga majalisar wakilai ta tarayya kan sauya sheka da daya daga cikinsu ya yi


Ƴaƴan jam’iyar PDP dake majalisar wakilai tarayya sun fice daga zauren majalisar kan sauya sheka da wani wakili daga jihar Imo Nnanna Igbokwe yayi.

Wasikar da Igbokwe ya rubutawa jam’iyar APC wacce kakakin majalisar Yakubu Dogara ya karanta a zauren majalisar kana ya kuma ta amince da sauya shekar a nan take.

Yin haka da kakakin majalisar yayi ya harzuka da dama daga cikin yan majalisar da suka fito daga jam’iyar adawa ta PDP inda suka nuna adawar su a fili ga matakin yayin da wasu kuma suka fice daga zauren majalisar.

Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha ya kasance a zaman majalisar na yau domin ya sheda sauya shekar Igbokwe  zuwa jam’iyar APC.

Igbokwe na wakiltar mazabar Mbese/Ezihinite a majalisar ta wakilai

You may also like