Yayan Kungiyar Boko Haram Sun Yanka Mutane 11 A Sansanin Yan Gudun Hijira Ranar Sallah 


Yan ta’addar kungiyar Boko Haram sun kashe mutane 11 suka kuma jikkata biyu a sansanin yan gudun hijira dake garin Banki  na kan iyakar Najeriya da Kamaru.

An rawaito cewa yan kungiyar sun shiga cikin sansanin dake dauke da mutane 45,000 inda suka kai hari, har takai da kisa da kuma jikkata wasu  ta hanyar yin amfani da wuka wajen kai harin.

Sun bi hanyar amfani da wuka wajen yin kisan ne   mai makon bindiga da kuma bama-bamai saboda kada sojojin dake aikin samar da tsaro a wurin su farga da abinda ke faruwa.

Amma kuma an sanar da sojojin  bayan da daga bisani aka gano abinda yafaru inda suka shiga farautar maharan.

Garin na Banki dai  ya fuskanci hare-hare da dama daga yayan kungiyar ta Boko Haram.  

You may also like