Yeman: Jiragen Yakin Saudiyya Sun Kai Hare-hare A San’aa.


Harin Saudiyya A birnin Sanaa.

Jiragen yakin Saudiyya sun kai hari a babban birnin kasar Yeman, San’aa.

Haren-haren na jiragen saudiyya sun shafi yankin Bani Bahlul a cikin babban birnin. Fararen hula da dama ne su ka rasa rayukansu sanadiyyar harin, wasu kuma da dama suka jikkata.

A gefe daya, sojojin kasar da kuma dakarun sa kai na Ansarulla, sun maida martani ya hanyar kai hari a sansanonin sojojin Saudiyya a kudancin kasar.

Fiye da watanni 20 kenan da Saudiyya ta shelanta yaki akan kasar Yeman da al’ummarta wanda kawo ya zuwa yanzu ya ci dubban rayuka.

You may also like