A kasar Kamaru, ‘yan fashi da makami sun kashe wani mutum 1 tare da yin garkuwa da wasu 6.
cewar kwamanda Yende Godfrey ,shugaban bataliyar sojojin kamaru ta 31 wadda ke a yankin Tchollire, a daren Juma’ar nan da ta gabata ce, wasu da ba’a san ko su waye ne ba, suka farwa mazauna garin Mbousiki na jihar Mayo Rey.
Ya zuwa yanzu babu wanda ya dauki alhakin aikata wannan ta’asar wadda ta haifar da fargaba a zukatan al’umomin jiha mafi girma ta Kamaru.Duk da jami’an tsaron kasar,na zargin wasu tsaffin ‘yan tawayen kasar afirka ta tsakiya.
Yende ya ce watanni 2 kenan da shugaban kasar Kamaru Paul Biya ya umarce su da tsaurara matakan tsaro a jihar Mayo Rey, saboda irin yadda masu fashi da kamami,’yan bindiga dadi,masu garkuwa da jama’a da kuma sauran ‘yan tada zaune tsaye ke ci gaba da addabar wannan yankin.
Da yake jan hankalin jama’ar Mayo,kwamandan ya ce sun gano da cewa wasu daga cikin al’umar wannan yankin na taima wa tsegerun.
Fashi da makami da kuma garkuwa da jama’a ababe ne da suka zama ruwan dare gama duniya a yankin Mayo Rey wanda ke kan iyakokin kasashen Cadi da na Afirka ta tsakiya.