A Yi Wa Barayin Gwamnati Afuwa – Dino Malaye


 

 

 

Sanata mai wakiltar jahar Kogi ta yamma Dino Malaye ya baiwa shugaban kasa shawarar cewa ya kafa shirin afuwa ga barayin gwamnati wadanda ake tuhuma da wadanda ba’a fara tuhuma da zai shafe watanni shida.

Ya fadi haka ne a sakon sa na ranar zagayowar ranar samun ‘yancin kai da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, inda ya rubuta cewa wannan al’amari zai janyo hankalin wadanda suka saci kudaden gwamnatin su dawo da su ga gwamnatin.

Ya ce shirin wanda ya kamata ya shafe watanni 6 zai bayarda afuwa ne ga duk wanda ya dawo da kudaden gwamnatin a cikin watanni shidan da gwamnatin ta ware.

 

Ya kara da cewa wannan zai taimaka wajen rage radadin tabarbarewar tattalin arzikin da kasar ke fuskanta -musammam ma ga talakawa tunda gwamnati za ta iya amfani da kudaden wajen fara ayyuka da za su inganta rayuwar su.

A karshe ya ce wannan matakin ya fi wanda gwamnatin ke dauka a yanzu na bibiyar mutanen da hukumomin tsaro da gurfanar da su a gaban kuliya bayan an san cewa za su iya sayen lauyoyin da za su iya dakile tafiyar shari’a su yi ta jan ta domin tabbatar da cewa uwayen gidansu sun kaucewa shari’a.

You may also like