An yi wa sojin Najeriya Kwanton bauna


c517eaa1651d080f7d3a76055bd6c83716b9703f

 

Rundunar Sojin Najeriya ta ce mayakan kungiyar Boko Haram sun yiwa sojojinsu kwantar bauna akan hanyar Damboa zuwa Maiduguri inda suka kashe fararen hula 6.

Daraktan yada labaran rundunar, Kanar Sani Usman Kukasheka, yace sojojin na rakiyar tawagar motocin sufuri ne lokacin da aka kai musu harin.

Jami’in yace sojojin su 3 sun samu rauni kuma an dauke su zuwa Maiduguri domin kula da lafiyar su.

Daraktan ya bukaci jama’a da su dinga taka tsan tsan, yayin da ya sha alwashin cewar sojojin zasu ci gaba da iya kokarinsu wajen murkushe mayakan.

You may also like