An yi watsi da ƴan jam’iyar APC na Taraba-Aisha Alhasan


Aisha-alhassan

Ministar al’amuran mata da cigaban jama’a Hajiya Aisha Jummai Alhasan tayi zargin cewa gwamnatin APC ta shugaban ƙasa Muhammadu Buhari tayi watsi da ƴan jami’iyar APC da suka fito daga jihar Taraba.
Alhasan tayi wannan zargin ne lokacin data jagoranci ƴaƴan jam’iyar APC na jihar zuwa Sakatariyar Uwar jam’iyar APC ta ƙasa.
“Nazo ne matsayina na ƴar jam’iyar APC tare da ƴan uwana daga Taraba mu bayyana matsalolin mu, mutanen APC a Taraba sun damu matuka”tace
“Babu wata jam’iyar adawa tun daga 1999 da tayi ƙoƙarin da mukayi,Amma abin takaici, banda muƙamin da aka bani na minista wanda kundin tsarin mulki yace abawa Ko wace jiha,sai muƙamin jakada, har yanzu babu wani muƙami da aka bamu”
Taƙara da cewa ƴan jam’iyar da suka bautawa jam’iyar sun yi tsammanin shugabannin su zasu taimaka musu wajen sama musu mukaman siyasa.
Ministar tace APC a Taraba tana da ƙwararrun mutane da zasu iya taimakawa gwamanatin tarayya a burinta na kawo canji da cigaban ƙasa idan aka basu mukami.
Dole mu Kula da mutanen mu , idan ba haka ba bamu san makomar mu ba zaben 2019. Koh aiyukan da gwamnatin tarayya takeyi  ba’a haɗawa damu.
Alhasan taƙara da cewa lallai yakamata a tuna da ƴan jam’iyar APC na jihar.
Mataimakin shugaban Jam’iyar shiyar arewa Lawal Shuaibu wanda ya karɓi tawagar, ya tabbatar musu cewa za’ayi maganin korafin su.
Shuaibu ya kuma shawarci ƴan jam’iyar, dama ƴan Najeriya baki ɗaya dasu ƙara haƙuri.

You may also like