An Yi Zanga Zangar Adawa Da Hukuncin Sakin El-Zakzaky


Wasu kungiyoyi masu zaman kansu sun mamaye Babban kotun tarayya da ke Abuja inda suka nuna rashin jin dadinsu game da hukuncin da kotun ta yanke da ke bukatar a saki shugaban kungiyar shi’a Ibrahim El Zakzaky.

Kungiyoyin sun gudanar da zanga zangar ne dauke da kwalaye masu rubutun sakonnin neman a tsige alkalin da ya zartar da hukuncin, kamar su ” Dole Kolowale ya tafi, Mun gaji da hukuncin banza”.

Masu zanga zangar sun nuna alhininsu game da abun da hukuncin ka iya haifarwa, inda suke ganin sakin El Zakzaky zai jefa jami’an tsaron kasar nan cikin hadari kuma zai halatta ayyukan ta’addanci a kasa.

Shugaban kungiyar Comrade Okpokwu Ogenyi ya ce kotun ta yi kuskure domin kuwa ta halalta ta’addanci ta kuma sanya sauran ‘yan Nijeriya cikin hatsari.

A makon da ya gabata ne dai Alkali Gabriel Kolawale na babban kotun tarayya da ke Abuja ya bayarda umarnin a saki shugaban na shi’a Ibrahim El-Zakzaky da shi da matarsa da ga gidan yari.

You may also like