Al’uma a birnin Chicago na Amurka sun gudanar da zanga-zanga sakamakon kama wani bakar fata Paul O’Neal tare da kashe shi da jami’an ‘yan sanda suka yi a ranar 28 ga watan Yuli.
Tun daga ranar da lamarin ya faru har zuwa yau al’umu daban-daban ne suke halartar zanga-zangar da ake shiryawa.
Daruruwan mutanen sun rufe manyan hanyoyi da gadojin birnin na Chicago.
Mutane sun taru a dandalin Karni tare da yin tattaki har na tsawon awanni 4 da nufin nuna rashin amincewa da halayyar ‘yan sanda.
Jama’ar sun nemi da a yi adalci game da kisan na Paul O’Neal wanda suka ce ‘yan sanda masu nuna wariyar launin fata ne suka kashe shi.
Mutanen sun dinga daga hotunan matashin da ‘yan sandan suka kashe inda suka dinga cewa, rayuwar bakar fata ma na da muhimmanci.
Sanarwar da ‘yan sandan suka fitar ta ce, a ranar 28 ga watan Yuli ya saci wata babbar mota inda ‘yan sanda suka bi shi da harbi wanda sakamakon haka ya rasa ransa.