An yiwa Jaririya ƴar wata bakwai fyade


download (1)

Wata yarinya ƴar watanni bakwai na can cikin mawuyacin hali a asibitin Haihuwa da kula da Yara na Turai Ƴar’adua dake Katsina, bayan da aka zargi mijin mahaifiyarta mai suna Magaji Dansade da yi mata fyade
Dansade ya aikata wannan mummunan aiki ne a gidan aurensu, dake ƙyauyen Dangaske a ƙaramar hukumar musawa ta jihar Katsina.
Mahaifin yarinyar yace bukatarsa shine a ceci rayuwar ƴarsa sannan a hukunta Dansade domin hakan ya zama izina ga masu shirin aikata laifi makamancin haka anan gaba
Tuni ƴan sanda suka tsare mai laifin, da aka tuntubeshi mai magana da yawun rundunar ƴansanda ta jihar Isa Gambo yace kwamishinan ƴansanda na jihar zaiyi karin bayani akan batun gobe juma’a.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like