Yiyuwar dawo da hukuncin kisa a Turkiya


 

Shugaba Recep Tayeb Erdogan ya ce, da yiwuwar Majalisar Dokokin kasar ta yi nazari kan sake dawo da hukuncin kisa bayan faruwar wannan juyin mulkin da ya yi sanadiyar asarar rayuka mutane 265.

Gwamnatin Turkiya ta zafafa bincike da nufin gano mutanen da suka shirya wa shugaban kasar juyin mulki a ranar juma’a, inda ta sanar da tsare mutane akalla dubu 6 kamar yadda , Ministan shariar kasar Bekir Bozdag ya bayyana a wata hira da aka yi da shi ta kafar talabijin din kasar.

Shugaba Erdogan ya lashi takobin ganin bayan duk wanda ke da hannu a abun da ya kira kokarin wargaza demokradiya, al’ummar kasar na ci gaba da nuna goyon baya ga shugaba Erdoghan a yayin da shugaban ya bukaci al’umma da su hada kai wuri guda don adawa da  daidaikun mutanen dake son tayar da zaune tsaye.

Al’ummar kasar sun taka muhinmiyar rawa wajen dakile juyin mulkin na makon da ya gabata.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like