Yunkurin samun tsagaita wuta a Ukraine


 

Ministocin harkokin wajen Jamus da Faransa sun kai ziyara a kasar don farfado da shirin tsagaiata wuta da aka cimma tun bara amma fada ya ci gaba tsakanin gwamnati da ‘yan awaren gabashin kasar.

 

Jean-Marc Ayrault da ke zama ministan harkokin wajen Faransa da takwaransa Frank-Walter Steinmeier na Jamus tare da shugaban kasar ta Ukraine Petro Poroshenko, za su duba yadda za su farfado da shirin tsagaita wutan. Kazalika za su duba yadda za’a kai ga kammala wasu tsare-tsaren siyasa da aka cimma a yarjejeniyar ta Minsk. A bangarensu ‘yan aware tun a ranar Talata, suka sanar da tsagaita wuta. Haka kuma ministan harkokin wajen Jamus ya ce ita gwamnatin Ukraine ta yi alkawarin fara aiki da tsagaita wutar tun a tsakiyar daren jiya Laraba.

You may also like