Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tattauna da Sarkin Saudiyya Salman Bin Abdulaziz a ranar Lahadin nan inda ya bayyana goyon bayan kasarsa ga Saudiyya game da yunkurin kai wa Makka hari da makami mai linzami da ta’addar Shi’ar Houthi da ke Yaman suka yi.
Buhari ya la’anci harin inda ya ce, wannan aiki ne na ‘yan ta’adda saboda an hari kasa mai tsarki wadda miliyoyin Musulmai suke halartadon gudanar da ibada.
Sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar na cewa, Buhari ya nuna farin cikinsa kan yadda jami’an tsaron Saudiyya suka kare kasar daga harin a makami mai linzami daga kasar Yaman bayan tare makamin a wuri mai nisan Kilomita 65 daga Makka.
Shugaba Buhari ya bayyana bukatar da ke akwai na a kara hada kai waje daya domin yaki da ta’addanci a duniya.