Yunwa na kara ta′azzara a duniya | Labarai | DWMutane miliyan 48 ne ke fama da matsalar yunwa sakamakon matsalar canjin yanayi a wasu kasashen duniya, in ji wani rahoton da kungiyar agaji ta Oxfam ta fitar a wannan Jumma’a.

Rahoton yace barazanar karancin kalacin na dada karuwa a wasu kasashe shida, da suka hada da Somaliya, Haïti, Djibouti, Kenya, Afghanistan, Guatemala, Madagascar da Zimbabwe da Nijar da kuma Burkina Faso, adadin da ya kara linkawa idan aka kwatanta da na miliyan 21 da aka samu a baya, a shekarar 2016.You may also like