Zaɓe Ya Gabato: An Tsinci Gawar Wani Almajiri A Katsina


An tsinci gawar wani yaro mai kimanin shekaru sha biyu da haihuwa a unguwar Kwado bayan filin wasan kwallon kafa na Muhammadu Dikko a garin Katsina.


A tattaunawar da wakilinmu ya yi da malamin da ke kula da yaron, Alaramma Malam Abubakar wanda aka fi sani da Alaramma mai lafiya Wurma wanda a cewarsa ya fito ne daga karamar hukumar Kurfi, amma yana zaune a unguwar ta Kwado da almajiransa, ya sheda bayanin yadda abin ya faru da cewa a ranar Litinin din da ta gabata ne bayan sun tashi daga karatun dare sai aka fara tambayar da wa da wa ke baya nan kamar yadda ya saba duk dare sai ya tambaya don ya ji kowa ya dawo kafin ya kwanta bacci. To amma sai ya samu labari daga abokan karatun yaron cewa ba a san inda ya shiga ba kuma sun duba ko ina ba su gan shi ba.

A haka dai suka yi ta neman sa har karfe daya na dare inda daga bisani malamin ya ce kowa ya je ya kwanta in gari ya waye sai a bincika kila ko ya bi wasu almajirai a makarantarsu ya kwana a can.

Alaramma Wurma ya ci gaba da cewa ana cikin jimamin rashin ganin yaron ne bayan gari ya waye sai ga daya daga cikin abokansa da su ke bara tare ya na kuka ya ce ya gan shi kwance an yanka masa ciki. Inda a nan take aka je wurin da gawar yaron ta ke suka kuma kirawo hukumar ‘yan sanda domin sanar da su halin da ake ciki.

Daga karshe Alaramma Abubakar ya ce likitoci sun duba gawar yaron kuma ba su ga alamar an cire wani abu a jikinsa ba.

Saidai ga dukkanin alamu ga jikin gawar yaron akwai alamun yin amfani da wani abu dake nuna an shakare shi kafin yanka masa cikin.

A dayan bangare kuma mutanen unguwar da aka tsinci gawar yaron suna kokawa dangane da halin ko inkula da masu rike da madafun iko suka yi, inda a cewarsu inda dan wani mai fada a ji ne da yanzu an hana su ko runtsawa.

Tuni dai aka yi wa yaron sutura kamar yadda musulunci ya tanada.

You may also like