Zaɓen 2023: Amnesty ta aike da gargaɗi mai karfi kan razana masu zaɓe
0
Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar Amnesty International ta ce dole ne hukumomin Najeriya da jam’iyyun siyasar ƙasar da ‘yan takara su fito fili su yi alla-wadai da masu kalaman nuna ƙiyayya da tunzura tashin hankali da kuma razana masu zaɓe.
Ta ce ba za a lamunci yadda wasu ‘yan siyasa da idonsu ya rufe, ke ingiza tashin hankali da neman a kai wa abokan hamayya hare-hare a lokutan yaƙin neman zaɓe ba.
Amnesty na wannan kira ne, kwanaki kaɗan a fita rumfunan zabe domin kada kuri’ar zaɓen shugaban ƙasa.
‘Gazawar hukumomi’
Ƙungiyar Amnesty International ta ce gazawar hukumomi wajen gurfanar da mutanen da suka tunzara miyagun rikice-rikice a zaɓukan baya a kotu, ta haifar da wani yanayi na aikata laifi da gadara da kuma zuga wasu.
Ta ce dole ne jam’iyyun siyasa da ‘yan siyasa da jami’an tsaro su daina lamunta ko shiga, ko tayar da hankali ko tunzara tashin hankalin da ke iya tauye ‘yancin ɗan adam.
Sanarwar ƙungiyar ta ce dole ne zaɓukan shugaban ƙasa da ‘yan majalisun tarayya na ranar 25 ga wannan wata, su kasance ba tare da tarzoma ko razanarwa ba, kuma jazaman a ɓullo da matakan kare duk masu ruwa da tsaki a harkar zaɓe da kuma hana keta ‘yancin bil’adama.
Skip Zaben Najeriya 2023: Waɗanne alƙawura ne jam’iyyu suka yi muku
Zaben Najeriya 2023: Waɗanne alƙawura ne jam’iyyu suka yi muku
Tsare tsaren Jam’iyyu
All Progressives Congress
Manyan muradu
Bunƙasa fitar da kaya daga Najeriya da kuma rage dogaro kan shigo da kaya
Rage adadin matasa marasa aikin yi da kashi hamsin cikin ɗari a cikin shekara huɗu da kuma samar da ayyuka miliyan ɗaya a ɓangaren sadarwa na zamani.
Ɗaukar matakan tabbatar da cin gashin kan ɓangaren shari’a ta fannin kuɗi da gudanarwa.
Tattalin arziki
Tallafa wa masana’antun cikin gida ta hanyar sauƙaƙa musu kuɗin haraji.
Kula da farashin kaya domin rage hauhawar farashi
Cire tallafi kan gas cikin wata shida da kuma ƙara yawan gas ɗin da ake samarwa da kashi 20%.
Aikin yi
Samar da ayyuka miliyan guda ta ɓangaren sadarwar zamani a cikin watanni 24 na farkon gwamnati.
Rage adadin matasa marasa aikin yi da kashi hamsin cikin ɗari a cikin shekara huɗu.
Tallafa wa masu sana’a miliyan biyu da kuma ƙwararru domin horas da matasa hanyoyin samun aiki da fara kasuwanci.
Kiwon lafiya
Aiwatar da shirin inshorar lafiya na tilas wanda kashi 40 cikin 100 na jama’a za su amfana a cikin shekara biyu.
Ƙara adadi da kuma inganta ma’aikatan lafiya musamman waɗanda suke aiki a matakin farko.
Aiki tare da gwamnatin jihohi da ƙananan hukumomi don samar da asibitocin tafi da gidanka domin tabbatar da cewa kowa na da asibiti aƙalla kilomita uku a kusa ko kuma tafiyar minti 30.
Ƙarfafa gwiwa don samar da magunguna da rigakafi a cikin Najeriya.
Tsaro
Ƙara Inganta albashi da walwalar ma’aikatan tsaro da kuma samar da wani shiri na musamman domin bayar da alawus ga sojoji da suka samu rauni da kuma waɗanda suka rasu a kan aiki.
Samar da makamai masu inganci, da inganta ɓangaren sadarwa da sufuri a sansanonin sojoji.
Ƙara dauka da horas da sabbin ma’aikatan soji da ƴan sanda da jami’an tsaron sirri da sauran masu kayan sarki.
Kawar da kai hare-hare kan muhimman wurare na gwamnati
Ilimi
Samar da sabbin hanyoyin tantance ingancin duka cibiyoyin ilimi tun daga firamare har zuwa jami’a.
Samar da shirin gwaji na bayar da bashi ga ɗalibai.
Samar da wani asusun ɗalibai na musamman wanda babu lamunin gwamnati a ciki.
Cin hanci da rashawa
Ƙayyade adadin kuɗaɗen da za a iya kashewa kan samar da gine-ginen gwamnati da albashi da kuma kan zaɓaɓɓun shugabanni da ma’aikatan gwamnati.
Ƙara samar da haraji ta hanyar rage kuɗaɗen da suke zurarewa daga ɓangaren kuɗin.
Saka wa masu aiki tuƙuru da kawar da ayyuka da ma’aikatan bogi.
Kawo sauyi ɓangaren aikin gwamnati domin rage abubuwan da ke kawo cikas, ko rashin ingancin aiki, da kuma ɓarna.
Labour Party
Manyan muradu
Gudanar da sauye-sauye a aikin gwamnati da ɓangaren shari’a domin tabbatar da bin doka, da yaƙi da rashawa da kuma tsimin kuɗi wurin tafiyar da gwamnati.
Mayar da Najeriya ƙasar da ke sana’anta abubuwan buƙata a maimakon sayowa daga wasu ƙasashe.
Fifita bunƙasa al’umma ta hanyar zuba jari a ɓangaren ilimin kimiyya da lafiya, abubuwan kawo ci gaba.
Tattalin arziki
Ɗora tattalin arziƙin Najeriya a kan tafarkin ƙirƙira da samar da kamfanoni ta yadda ƙasar za ta rinƙa fitar da kaya zuwa waje.
Rage tashin farashin kaya, da tabbatar da cin gashin kai na babban bankin ƙasar, da kyautata tsarin biyan haraji.
Rage dogaron da Najeriya ke yi kan man fetur ta hanyar inganta ɓangaren masana’antu.
Sassauta takunkumi kan kayan da ake shigowa da su daga ƙasashen waje da canjin kuɗi, tare kuma da samar da tsarin musayar kuɗi guda ɗaya.
Aikin yi
Faɗaɗa hanyoyin samar da kuɗi ga ƙanana da matsakaitan sana’o’i, da mata da matasa domin rage matsalar rashin aikin yi.
Zuba jari a ɓangaren bunƙasa al’umma.
Inganta hanyar sauƙaƙa yin kasuwanci a ƙasar domin janyo masu zuba jari ta yadda za a samar da kamfanoni.
Samar da yanayi mai kyau na bunƙasar ƙananan sana’o’i.
Kiwon lafiya
Inganta albashi da kuma yanayin aikin ma’aikatan lafiya.
Samar da inshorar lafiya ga talakawan Najeriya miliyan 133, musamman mata masu ciki, da yara, da tsofaffi da kuma masu lalurar nakasa.
Ƙara wa malaman lafiya ilimi ta hanyar bayar da horo.
Samar da kiwon lafiya mai sauƙi ga kowa.
Tsaro
Kawo ƙarshen ayyukan ƴan bindiga da na masu tayar da ƙayar baya.
Haɗa kai da ƙasashen yammaci da na tsakiyar nahiyar Afirka domin inganta tsaro na kan iyaka, musamman ƙasashen Chadi da Jamhuriyar Nijar, da Kamaru.
Haɗa hannu da majalisar dokoki domin samar da jami’an tsaro na cikin al’umma.
Ƙara yawan jami’an soji, da ƴan sanda da sauran hukumomin tsaro, da samar masu da kayan aiki, da ba su horaswa, da samar masu da kuɗaɗe ta yadda za su iya magance barazanar tsaro.
Ilimi
Zuba jari a ɓangaren koyar da sana’o’i, da wasannin motsa jiki, da horaswa kan ilimin fasahar zamani daga makarantun firamare zuwa sakandare.
Tsarin ilimi wanda ‘ba za a bar kowane yaro a baya ba’
Samar da tsarin biyan harajin kamfanoni ta hanyar kula da makarantu mallakin gwamnati, samar da tsarin karatu da kula da ayyukansu.
Ware kashi 14% na kasafin kuɗi ga ɓangaren ilimi.
Cin hanci da rashawa
Yin biyayya ga dokoki na tsarin kuɗi.
Binciken harkokin kuɗi na kowane fallen gwamnati a kai-a kai
Toshe duk wasu hanyoyin zurarewar kuɗi da kawo ƙarshen tallafin man fetur.
Tafiyar da lamurran gwamnati a bayyane.
New Nigeria Peoples Party
Manyan muradu
Samar da ayyukan yi ta hanyar bunƙasa noma.
Magance matsalar tsao.
Martaba doka da bin ƙa’ida.
Tattalin arziki
Yaƙi da rashawa a ma’aikatu da hukumomin gwamnati domin bunƙasa kuɗaɗen shiga.
Kawo sauyi a kasuwar hannayen jari ta ƙasar domin inganta ta ta yadda za ta zamo hanyar samun kuɗaɗen kasuwanci.
Neman ingantacciyar hanyar tafiyar da kasuwar musayar kuɗi.
Aikin yi
Zaftare yawan marasa aikin yi.
Ƙarfafa wa matasa gwiwa domin shiga harkar noma.
Ƙarfafa wa ɓangaren ƴan kasuwa gwiwa domin su kafa kamfanonin sarrafa amfanin gona domin samar da aikin yi ga matasa.
Kiwon lafiya
Kawo sauyi a shirin inshorar lafiya na ƙasa.
Rage yawan tafiye-tafiye zuwa ƙasashen waje domin neman lafiya, ta hanyar bunƙasa asibitoci, da bunƙasa yadda ake gudanar da aiki, da bayar da horo ga ma’aikatan lafiya.
Samar da ƙarin kuɗi ga ɓangaren kiwon lafiya a cikin kasafin kuɗi.
Tsaro
Samar da isassun kayan aiki da tattara bayanan sirri domin magance matsalar tsaro.
Bunƙasa fahimtar juna da yafiya a tsakanin al’umma.
Yi wa al’umma cikakken bayani kan ayyukan gwamnati.
Ilimi
Samar da isassun kuɗi ga ɓangaren ilimi.
Bunƙasa manyan makarantu kafin samar da sabbi.
Tallafa wa ƙananan hukumomi domin su iya samar da muhalli ga yara sama da miliyan 20 waɗanda ba su zuwa makaranta kuma suke yawo kan titi.
Cin hanci da rashawa
Sauyawa da ƙarfafa hukumomin yaƙi da rashawa.
Tafiyar da ayyukan gwamnati cikin adalci.
Amfani da fasahar zamani domin daƙile ayyukan rashawa.
Peoples Democratic Party
Manyan muradu
Bai wa masana’antu masu zaman kansu fifiko wurin haɓɓaka tattalin arziki.
Ƙara haɗa kan ƴan ƙasa ta hanyar yin raba-dai-dai tsakanin yankunan ƙasar a wurin bayar da muƙamai.
Sauya fasalin gwamnatin Najeriya
Tattalin arziki
Tabbatar da cewa Najeriya ta ci gaba da zama giwar Afrika da tabbatar da cewa ma’aunin GDP ya ruɓanya zuwa $5,000 zuwa 2030.
Haɓɓaka zuba jari ta ɓangaren ababen more rayuwa zuwa kaso 50 na ma’aunin GDP zuwa 2027, kaso 70 kuma zuwa 2023.
Ƙara yawan man fetur ɗin da ake tacewa zuwa ganga miliyan biyu a rana zuwa 2027.
Aikin yi
Samar da ayyukan yi miliyan uku da tsamo mutum miliyan goma daga talauci a duk shekara.
Ƙaddamar da shiri na musamman ingantacce mai rahusa kuma mai dorewa domin samar da aikin yi da kuma sana’o’i.
Samar da wuraren horaswa ga matsakaita da manyan masu sana’o’i.
Kiwon lafiya
Ƙara hanzarta shirin Najeriya na samar da ingantaccen kiwon lafiya kuma mai sauƙi zuwa 2030.
Jawo hankalin likitocin Najeriya da ke ƙasashen waje su dawo gida.
Ƙarfafa gwiwar matsakaita da manyan kamfanonin samar da magunguna da su ƙara adadin magungunan da suke samarwa na cikin gida da ake nema.
Tsaro
Haɓɓaka rajistar haihuwa domin rage aikata laifuka da kuma kare ƴan Najeriya.
Ɗaukar jami’an ƴan sanda miliyan ɗaya domin cimma muradun MDD na kowane mutum 450 ɗan sanda 1.
Ƙara yauƙaƙa dangantaka tsakanin farar hula da sojoji.
Sauya fasalin cibiyoyin tsaro.
Ilimi
Ƙara haɓɓaka karatun kimiyya da fasaha domin samar da dabaru ga sabon tattalin arziki.
Samar da wata hukuma wadda za ta sa ido kan manyan makarantu.
Ƙara zuba jari ta ɓangaren ababen more rayuwa na gwamnatin tarayya da kuma jihohi.
Cin hanci da rashawa
Sake bitar tsarin saka wa ma’aikatan gwamnati masu ƙwazo.
Zamanantar da ayyukan gwamnati domin gano cin hanci.
Tabbatar da cewa hukumomin da suka dace sun aiwatar da hukunci da ake yankewa kan laifukan rashawa.
End of Zaben Najeriya 2023: Waɗanne alƙawura ne jam’iyyu suka yi muku
‘Cin zarafin jinsi’
Daraktar Amnesty a Nijeriya Osai Ojigho ta ce dole ne a dakatar da cin zarafin jinsi kamar yi wa mata da ‘yan mata barazanar fyaɗe don a razana su ko a hana su kaɗa ƙuri’a.
Ta ba da misali da wasu tashe-tashen hankula a ‘yan watannin nan kamar na 28 ga watan Nuwamban 2022, inda wasu ‘yan bindiga suka kasheVictoria Chimtez wata shugabar jam’iyyar Labour a jihar Kaduna da kashe Olumo Abolaji ta jam’iyyar APC a jihar Kwara bayan sace ta.
Sai jikkata gomman magoya bayan jam’iyyar PDP, ranar 9 ga watan Nuwamban bara, lokacin da aka kai wa kwambar yaƙin neman zaɓen Atiku Abubakar hari.
Osai Ojigho jazaman ne hukumomi su kawar da duk wani yunƙurin aikata laifi cikin gadara ta hanyar tabbatar da ganin an yi bincike kan tashe-tashen hankulan siyasa kuma a gaggauta daukar matakan shari’ah a kan mutanen da aka samu da hannu.
‘Ayyuka cikin aminci’
Amnesty International ta kuma ce dole ne a tabbatar ‘yan jarida da masu sa-ido kan zaɓuka na cikin gida da na ƙasashen waje da sauran masu ruwa da tsaki sun yi ayyukansu cikin aminci a lokacin zaɓuka ba tare da tsoron tashin hankali ko razanarwa ba.
Ƙungiyar ta ce za ta ci gaba da bibiya da kuma tattara bayanan duk wani aiki na keta ‘yancin ɗan’adam don tabbatar da ganin an hukunta mutanen da suka aikata, ko su wane ne su.