Ƙungiyar Amnesty International ta ce dole ne hukumomin Najeriya da jam’iyyun siyasar ƙasar da ‘yan takara su fito fili su yi alla-wadai da masu kalaman nuna ƙiyayya da tunzura tashin hankali da kuma razana masu zaɓe.
Ta ce ba za a lamunci yadda wasu ‘yan siyasa da idonsu ya rufe, ke ingiza tashin hankali da neman a kai wa abokan hamayya hare-hare a lokutan yaƙin neman zaɓe ba.
Amnesty na wannan kira ne, kwanaki kaɗan a fita rumfunan zabe domin kada kuri’ar zaɓen shugaban ƙasa.
‘Gazawar hukumomi’
Ƙungiyar Amnesty International ta ce gazawar hukumomi wajen gurfanar da mutanen da suka tunzara miyagun rikice-rikice a zaɓukan baya a kotu, ta haifar da wani yanayi na aikata laifi da gadara da kuma zuga wasu.
Ta ce dole ne jam’iyyun siyasa da ‘yan siyasa da jami’an tsaro su daina lamunta ko shiga, ko tayar da hankali ko tunzara tashin hankalin da ke iya tauye ‘yancin ɗan adam.
Sanarwar ƙungiyar ta ce dole ne zaɓukan shugaban ƙasa da ‘yan majalisun tarayya na ranar 25 ga wannan wata, su kasance ba tare da tarzoma ko razanarwa ba, kuma jazaman a ɓullo da matakan kare duk masu ruwa da tsaki a harkar zaɓe da kuma hana keta ‘yancin bil’adama.
‘Cin zarafin jinsi’
Daraktar Amnesty a Nijeriya Osai Ojigho ta ce dole ne a dakatar da cin zarafin jinsi kamar yi wa mata da ‘yan mata barazanar fyaɗe don a razana su ko a hana su kaɗa ƙuri’a.
Ta ba da misali da wasu tashe-tashen hankula a ‘yan watannin nan kamar na 28 ga watan Nuwamban 2022, inda wasu ‘yan bindiga suka kasheVictoria Chimtez wata shugabar jam’iyyar Labour a jihar Kaduna da kashe Olumo Abolaji ta jam’iyyar APC a jihar Kwara bayan sace ta.
Sai jikkata gomman magoya bayan jam’iyyar PDP, ranar 9 ga watan Nuwamban bara, lokacin da aka kai wa kwambar yaƙin neman zaɓen Atiku Abubakar hari.
Osai Ojigho jazaman ne hukumomi su kawar da duk wani yunƙurin aikata laifi cikin gadara ta hanyar tabbatar da ganin an yi bincike kan tashe-tashen hankulan siyasa kuma a gaggauta daukar matakan shari’ah a kan mutanen da aka samu da hannu.
‘Ayyuka cikin aminci’
Amnesty International ta kuma ce dole ne a tabbatar ‘yan jarida da masu sa-ido kan zaɓuka na cikin gida da na ƙasashen waje da sauran masu ruwa da tsaki sun yi ayyukansu cikin aminci a lokacin zaɓuka ba tare da tsoron tashin hankali ko razanarwa ba.
Ƙungiyar ta ce za ta ci gaba da bibiya da kuma tattara bayanan duk wani aiki na keta ‘yancin ɗan’adam don tabbatar da ganin an hukunta mutanen da suka aikata, ko su wane ne su.