
Asalin hoton, Getty Images
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa a Najeriya, ta yi alƙawari cewa a zaɓen 2023, kayan aiki ne za su jira masu zaɓe a rumfunan kaɗa ƙuri’a saɓanin yadda aka dinga samu a baya.
Shugaban INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu ne ya shaida hakan yayin wani taro don ƙulla yarjejeniya da ƙungiyoyin sufuri na NURTW da NARTO kan hanyoyin sauƙaƙa jigilar ma’aikata da kayan aikin zaɓe zuwa cibiyoyin zaɓe.
A cewar shugaban hukumar, sun yi waiwaye kan matsalolin da aka dinga fuskanta a zaɓen 2019, kuma hakan ya sanya su ɗaukar matakan riga-kafi daga manyan ƙalubalen da za su iya kawo cikas ga nasarar zaɓen shekara mai zuwa.
Ya ce hakan ba zai yiwu ba har sai INEC ta samu ƙarin motoci da babura da kwale-kwale musamman a yankunan da ke kusa da ruwa, inda isar ma’aikatan hukumar zuwa waɗannan wuraren a kan lokaci ke da wahala.
Babban zaɓen na baɗi zai ƙunshi aikin tura jami’an zaɓe sama da miliyan 1 a duk faɗin Najeriya da ɗumbin adadi na kayan aiki sau biyu a cikin mako biyu daga ofisoshin hukumar INEC na jihohi zuwa ƙananan hukumomi 774 da mazaɓu 8,809 da cibiyoyin zaɓe 176,846.
Gagarumin aikin, in ji sanarwar INEC zai buƙaci motoci sama da 100,000 da jiragen ruwa kimanin 4,200 waɗanda jiragen sojojin ruwa da aka girkawa bindigogi za su yi musu rakiya.
Ta ce wannan wani jan aiki ne da za a yi shi nan da kwana 66 kuma mun ƙuduri niyyar yin haka don bai wa ‘yan Najeriya damar yin zaɓe cikin farin ciki.
Farfesa Mahmud Yakubu ya kuma bai wa ‘yan Najeriya tabbacin cewa sun duƙufa wajen ganin an buɗe duk rumfunan zaɓe da ƙarfe 8:30 na safe ranar Asabar 25 ga watan Fabrairu don zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisun tarayya da kuma a ranar Asabar 11 ga watan Maris ɗin 2023 don zaɓen gwamna da na ‘yan majalisar dokokin jihohi.
A Shekarar 2015 ne INEC ta fara ƙulla yarjejeniya da ƙungiyar NURTW inda ta sake bibiyar yarjejeniyar a 2018 domin shigar da NARTO kuma hukumar ta dogara ne kan yarjejeniyar da ta ƙulla da su domin samar da motoci wajen jigilar ma’aikata da kuma kayan aiki zuwa wuraren da ake buƙata.
Sai dai a baya, hukumar ba ta sa ƙungiyar MWUN ta ma’aikatan jiragen ruwa a cikin yarjejeniyar ba lamarin da a mafi yawan lokuta ke haifar da matsaloli game da turawa da kuma kwaso ma’aikata da kayan aiki daga wuraren da ke kusa da ruwa.
“Hakan ne ya sa aka ƙara bibiyar yarjejeniyar don sanya su a cikin masu jigilar kayan aikin zaɓe zuwa cibiyoyin kaɗa ƙuri’a.”
Farfesa Yakubu ya kuma buƙaci ƙungiyoyin su tabbatar mambobinsu sun mutunta yarjejeniyar don kauce wa abubuwan da za su iya janyo tsaiko a ranar zaɓe.
Sai mai dakon kayan zaɓe ya rantse
Wani sabon tanadi a sabon tsarin dokar zaɓe shi ne duk mutumin da zai shiga cikin harkokin zaɓe, sai ya rantse zai kasance ɗan ba-ruwanmu.
Asalin hoton, INEC Facebook
INEC ta ce tana buƙatar ɗumbin ababen hawa kamar babura da babur mai ƙafa uku da jiragen ruwa da kwale-kwale saboda ita ba ta da su
Sanarwar ta ce don haka INEC za ta buƙaci ‘ya’yan ƙungiyar masu sufurin motar su yi rantsuwa kuma su tabbatar da cikakkiyar biyayya ga wannan rantsuwa da kuma tanade-tanaden kundin tabbatar da ɗa’ar ma’aikatan INEC don kuwa shigar su cikin aikin kai kayan zaɓe na buƙatar su kasance cikakkun ‘yan ba-ruwanmu waɗanda kuma babu ruwansu da kowacce jam’iyya.
Haka zalika, hukumomin tsaro ba kawai za su kasance wajen raka dukkan motoci da jiragen ruwa zuwa wuraren da aka tura su ba, za kuma su tabbatar da kariya da tsaron lafiyar dukkan jami’in zaɓe da kayan aiki.
Kuma kamar yadda aka saba, hukumar INEC ta ce ta riƙa bin sawun duk wani abin hawa da jiragen ruwa ta hanyar latroni kuma kai tsaye don tabbatar da ganin ba a karkatar da jami’ai ko kayan zaɓe ba.
Asalin hoton, INEC Facebook
Kwafi-kwafi na yarjejeniyar da INEC ta sa hannu da ƙungiyoyin masu sufurin motoci a Najeriya