
Asalin hoton, AFP
A wata mai zuwa ne ƴan Najeriya za su je rumfunan zaɓe domin gudanar da zaɓen shugaban ƙasa duk da halin duk da ake ciki na rashin jin daɗi sakamakon matsalolin tsaro da kuma matsin tattalin arziki.
Shin ko ɗaya daga cikin waɗanda ke kan gaba a neman kujerar shugaban ƙasar waɗanda suka shafe shekaru a fagen siyasa za su iya kawo sauyi?
Daga tashin farashi zuwa hare-haren ƴan bindiga kan farar hula, mulkin Shugaba Buhari wanda a halin yanzu ya shafe kusan shekara takwas ya gamu da ƙalubale daban-daban.
Magoya bayansa sun bayyana cewa ya yi iya ƙoƙarinsa inda suka lissafo irin nasarorin da ya samu, misali irin ayyukan da ya yi na more rayuwa da kuma matakan da ya ɗauka domin daƙile masu tsatsauran ra’ayi.
Sai dai ko mai ɗakinsa Aisha Buhari ta bayar da haƙuri ga ƴan Najeriya kan sun gaza biyan wasu buƙatun ƴan ƙasar.
A halin yanzu duk wanda ya ci zaɓe, yana da jan aiki a gabansa.
Yaushe ne zaɓen?
Ana sa ran gudanar da zaɓen a ranar Asabar 25 ga watan Fabrairun 2023. Idan ba a samu wanda ya ci zaɓen ba, za a je zagaye na biyu wanda za a agudanar bayan makonni uku.
Haka kuma za a gudanar da zaɓen gwamnoni a ranar 11 ga watan Maris.
Shugaban hukumar zaɓe INEC ya yi watsi da ce-ce-ku-cen da ake yi kan cewa akwai yiwuwar ɗage zaɓen saboda dalilai na tsaro.
Su wa ke takarar shugaban ƙasa
Jimillar mutum 18 ne ke fita yaƙin neman zaɓe domin neman kujerar shugaban ƙasa, sai dai mutum uku ne ake ganin suna kan gaba a ra’ayoyin jama’a.
Bola Ahmed Tinubu mai shekara 70, shi ne ɗan takarar jam’iyya mai mulki ta APC.
An san shi a matsayin uba a siyasa a kudu maso yammacin Najeriya, yana da ƙarfin faɗa a ji matuƙa sai dai ana yi masa zarge-zargen cin hanci da rashawa a tsawon shekaru kuma ana zargin ba shi da isassar lafiya, sai dai duk ya musanta waɗannan zarge-zargen.
Wasu na cewa taken yaƙin neman zaɓen Emi Lokan, wanda yake nufin “lokacina ne[na zama shugaban ƙasa]” a Yarabanci, yana nuna wata alama ta isa.
Atiku Abubakar, mai shekara 76, shi ne yake takarara a babbar jam’iyyar adawa ta Najeriya wato PDP.
Wannan ce takara ta biyar da yake fitowa ta shugaban ƙasa – kuma duk waɗanda ya fito a baya bai yi nasara ba.
Akasarin ayyukan da ya yi suna da alaƙa da mulki, bayan ya yi aiki a matsayin ɗaya daga cikin manyan ma’aikata na Najeriya, ya zama mataimakin shugaban ƙasa a ƙarƙashin mulkin Olusegun Obasanjo sa’annan ya zama ɗan kasuwa.
Kamar dai Mista Tinubu, ana zargin Atiku da cin hanci da rashawa da azurta yan uwa da iyalai, inda duk ya musanta zarge-zargen.
Rabiu Musa Kwankwaso, mai shekara shekara 66, shi ne ɗan takarar jam’iyyar NNPP a Najeriya.
Kwankwaso, wanda ya yi gwamnan Kano tsakanin 1999 zuwa 2003 da kuma 2011-2015, yana da ɗumbin magiya baya musamman a jihar Kano waɗanda ake kira ƴan kwankwasiyya.
Sa’annan ya yi sanata tsakanin shekarar 2015 zuwa 2019.
Sai dai shi ma an sha gabatar da koke a kansa kan zarge-zargen cin hanci da rashawa musamman lokacin da yake gwamnan Kano kan batun kuɗin ƴan fansho.
Peter Obi mai shekara 61, yana da burin karya ƙwarin tsarin jam’iyyu biyu a Najeriya waɗanda suka yi kaka-gida a siyasar Najeriya tun bayan komawar mulki hannun farar hula a 1999.
Duk da cewa a baya yana a Jam’iyyar PDP ne, ana kallonsa a matsayin baƙuwar fuska kuma yana da magoya baya matuƙa a shafukan sada zumunta da kuma matasan Najeriya.
Ɗan kasuwa ne kuma ya taba zama gwamnan Jihar Anambra daga 2006 zuwa 2014.
Waɗanda ke mara masa baya waɗanda ake kira a matsain “OBIdients” sun ce shi ne kaɗai ɗan takara mai nagarta, amma masu caccakarsa na ganin zaɓen Obi kamar asarar ƙuri’a ce kuma babu alamun zai lashe zaɓe.
Wa ake ganin zai ci zaɓen?
Ana hasashen cewa ɗaya daga cikin ƴan takara daga manyan jam’iyyun ƙasar Atiku ko Tinubu ɗaya daga cikinsu zai ci zaɓen.
Sai dai masu goyon bayan Mista Obi na sa ran zai iya bayar da mamaki idan matasa za su iya jefa musu ƙuri;u masu yawa.
Ta yaya ake zaɓen?
Idan ana so a ci zaɓe, sai ɗan takara ya zama shi ke da mafi yawan ƙuri’u a faɗin ƙasa, kuma sai ya samu ɗaya bisa huɗu na jihohi biyu bisa uku na Najeriya.
Idan babu ɗan takarar da ya samu wannan, sai an je zagaye na biyu wanda za a gudanar cikin makonni uku tsakanin ƴan takara biyu waɗanda suka fi samun ƙuri’u.
Waɗanne matsaloli ne ke kan gaba?
Daƙile matsalar tsaro na daga cikin manyan abubuwan da masu zaɓe ke buƙata, a ƙasar da ake fama da garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa da kuma matsalar masu iƙirarin jihadi a wasu sassa na ƙasar.
Ɗaya daga cikin manyan hare-harenda aka samu a bara akwai batun kashe gwamman mutane da kuma sace kusan fasnjoji 100 da ke cikin jirgin ƙasan Kaduna zuwa Abuja.
Asalin hoton, AFP
Shugaba Buhari ya ce ya cika alƙawuran da ya yi wa yan Najeriya, sai dai da dama daga cikin ƴan ƙasar na ganin har yanzu akwai sauran rina a kaba.
Batun tattalin arziki ma wata matsala ce ta daban.
Domin kuwa a 2022, hauhawar farashi ya ƙaru na kusan watanni goma, inda har ya kai kashi 21.3, kamar yadda wasu bayanai da aka saki a wannan watan suka bayyana.
Wannan hauhawar farashin ya ja jama’a da dama suna ta ƙoƙari domin ganin sun biya wa kansu buƙatu.
Haka kuma batun rashin aikin yi wata matsala ce ta daban, inda take saka tsoro ko fargaba a zukatan ɗaliban da suka kammala jami’o’i kan cewa ba lallai su samu aikin da za su yi ba.
Shin za a yi zaɓe mai inganci?
A wasu zaɓukan da aka yi a baya a Najeriya, an rinƙa samun bayanai sahihai kan maguɗin zaɓe, ta hanyar haddasa rikici domin korar masu zaɓe ko kuma satar akwati da kuma cikasu bayan yin dangwale.
Sai dai hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta ce amfani da sabbin na’urori na kimiyya za su taimaka wurin tsare ƙuri’u.
Akwai kuma labarun da ake samu na ƴan siyasa suna biyan masu jefa ƙuri’a domin goya musu baya har a rumfar zaɓe.
Amma wani sauyi da aka yi kan takardar naira ya ja sayen ƙuri’a zai zama abu mai wahala, haka kuma jami’an tsaro za su kama duk wani mutum da zai bayar da kuɗi ko kuma karɓa.
Haka kuma INEC ta haramta wa masu zaɓe shiga da waya wuraren jefa ƙuri’a domin ɗaukar hoton ƙuri’arsu, inda akasari wakilan jam’iyyu na neman hakan a matsayin shaida.
An kai hare-hare wasu ofisoshin hukumar INEC. Ko a watan Nuwambar bara sai da INEC ɗin ta gudanar da wani taron gaggawa kan irin hare-haren da ake kai wa ofisoshinta .
Waɗanne zabuka ne kuma za a gudanar?
Bayan zaɓen shugaban ƙasa da za a agudanar, jama’a za su gudanar da zaɓen ƴan majalisar tarayyar ƙasar.
Akwai kujeru 469 waɗanda suka ƙunshi ƴan majalisar dattijai 109 da kuma na wakilai 360.
Bayan makonni biyu a ranar 11 ga watan Maris ake sa ran gudanar da zaɓen gwamnoni a cikin jihohi 28 cikin 36 na ƙasar.
Me ake nema domin jefa ƙuri’a
Idan mutum yana so ya yi zaɓe, yana buƙatar katin zaɓe na din-din-din wanda ake kira PVC wanda shi ne yake nuna mutum an yi masa rajista.
Asalin hoton, AFP
Katin zaɓen yana ɗauke da bayanai kan masu zabe kuma ana amfani da katin ne domin tantance mutum a ranar zaɓe.
Ana ajiye bayanan mutum a jikin katin. Idan mutum yana so ya yi amfani da katin domin jefa ƙuri’a sai ya je rumfar zaɓe tsakanin 8:00 na safe zuwa 14:00 na rana.
Muddin mutum yana kan layi har zuwa ƙarfe biyu na rana, za a bar mutum ya jefa ƙuri’a, kamar yadda hukumar zaɓe INEC ta bayyana.
Ba za a bar ƴan Najeriya da ke zaune a ƙasashen waje su gudanar da zaɓe ba.
Mece ce BVAS
Wannan zaɓen da ke tafe zai bambanta da sauran na baya sakamakon za a yi amfani da na’urar Bimodal Voter Accreditation System, wanda wata na’ura ce da INEC ta fito da ita a 2021 daƙile maguɗin zaɓe.
BVAS wata na’ura ce ƴar ƙarama kamar akwati da ke da sikirin wanda ya fi na’urar card reader ta tantance masu jefa ƙuri’a wadda ake amfani da ita a baya.
Amfanin BVAS shi ne za a iya amfani da na’urar wurin tantance mutum ta ɓangare biyu, za a iya tantance mutum ta zanen yatsunsa ko kuma ta fuskarsa.
Wannan matakin zai taimaka wurin dakatar da mutane waɗanda ba su da katin zaɓe daga jefa kuri’a
Yaushe za a samu sakamakon zaɓen?
A zaɓukan shugaban ƙasa biyu na baya da aka gudanar, an san wanda ya ci zaɓen a rana ta uku bayan zaɓen. Amma za a ci gaba da ƙidaya ƙuri’u da zarar an kammala zaɓe a ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu.
Waɗanda suka yi zaɓe a rumfunan zaɓe za a sanar musu da sakamakon zaɓen da suka yi a rumfa, amma akwai jan aiki kafin a kammala tattara sakamakon zaɓen a kai shi har zuwa Abuja babban birnin ƙasar.
Akwai yiwuwar BVAS ɗin zai taimaka wurin ƙara saurin tafiyar da zaɓen a bana, amma jami’an da INEC ta naɗa daga faɗin jihohi 36 na Najeriya za su yi takakkiya har zuwa Abuja domin su karanto sakamakon zaɓen kowa yana ji.
Bayan nan ne INEC ɗin za ta iya sanar da wanda ya ci zaɓen – ko kuma idan za a je zagaye na biyu.