
Asalin hoton, Getty Images
Paris St Germain za ta fafata da Bayern Munich ranar Talata a wasan farko a Champions league zagayen kungiyoyi 16 da suka rage a gasar.
Bayern za ta buga wasan ne, bayan karawa 19 a jere ba a doke ta ba – har da lashe wasa uku da ta buga a bayan nan.
Kungiyar Jamus ta kawo wannan matakin, bayan cin dukkan karawa shidan da ta yi a Champions League a kakar nan.
PSG da Bayern Munich sun sha haduwa a zagayen ‘yan 16 a Champions League.
Kaka ta 11 da PSG ke zuwa matakin ‘yan 16 a gasar zakarun Turai, Real Madrid da Bayern ne ke gabanta a wannan kwazon.
Rabon da Bayern ta kasa zuwa irin wannan matakin tun kakar 2007/08, ita kuwa Real kan je zagayen ‘yan 16 tun da aka kirkiro gurbin a 2003/04
Sai dai karo hudu ana fitar da PSG daga wasa shida baya a zangon ‘yan 16, ita kuwa Bayern sau daya ta kasa kai wa Quarter final daga fafatawa 10 a baya shine a 2018/19.
Bayern ta ziyarci Faransa ba tare da Sadio Mane da Lucas Hernández da Noussair Mazraoui da kuma Manuel Neuer, wadanda ke jinya.
Ryan Gravenberch ya warke, bayan da bai yi mata karawa da Wolfsburg da Bochum ba, Joshua Kimmich zai buga fafatawar, bayan dakatar da shi a Bundesliga.
Kyalian Mbappe wanda ya ci kwallo bakwai a cikin rukuni a Champions League a bana ya murmure, wanda aka ce zai yi jinya mai tsawo tun farko.
Kyaftin din Argentina, Lionel Messi yana cikin ‘yan kwallon da PSG ta bayyana da za su kara da Bayern ranar Talata.
Tsohon dan kwallon Bayern, Renato Sanches wanda ke taka leda a PSG na yin jinya.
Kungiyoyin sun kara a Champions League sau 11, inda PSG ta ci karawa shida, ita kuwa Bayern ta yi nasara a biyar.
Wasa 11 baya da aka kara tsakanin kungiyoyin biyu:
- Paris St-G. 0 – 1 Bayern Munich
- Bayern Munich 2 – 3 Paris St-G.
- Paris St-G. 0 – 1 Bayern Munich
- Bayern Munich 3 – 1 Paris St-G.
- Paris St-G. 3 – 0 Bayern Munich
- Bayern Munich 2 – 0 Paris St-G.
- Paris St-G. 1 – 0 Bayern Munich
- Paris St-G. 3 – 1 Bayern Munich
- Bayern Munich 5 – 1 Paris St-G.
- Bayern Munich 0 – 1 Paris St-G.
- Paris St-G. 2 – 0 Bayern Munich