
Asalin hoton, Getty Images
Ranar Asabar 11 ga watan Fabarairu za a ci gaba da wasannin mako na 23 a gasar Premier League, inda za a yi karawa bakwai.
Kawo yanzu an buga karawa 210 an kuma ci kwallo 576, kuma Erling Haaland na Manchester City shi ne kan gaba a zura kwallaye a raga mai 25.
Cikin wasannin da za a buga ranar Asabar Arsenal wadda take jan ragamar teburin a bana mai maki 50 za ta karbi bakuncin Brentford a Emirates, wadda take ta bakwai mai maki 33.
Za a fara ne da karawar West Ham United da Chelsea da tsakar rana, inda kungiyar David Moyes take ta 17 da maki 19.
Chelsea wadda ta kara cefane mai yawa a Janairun nan, tana ta tara a teburin babbar gasar tamaula ta Ingila da mai maki 30.
Wani wasan da zai ja hankali shi ne tsakanin Bournemouth, wadda take ta biyun karshen teburi da Newcastle, wadda take neman gurbin ‘yan hudu a bana.
Newcastle tana ta hudu a teburi mai maki 40, ita kuwa Bournemouth 17 ne da ita a mataki na 19 a babbar gasar tamaula ta Ingila.
Wasannin mako na 23 a Premier ranar Asabar.
- West Ham United da Chelsea
- Arsenal da Brentford
- Fulham da Nottingham Forest
- Southampton da Wolverhampton
- Leicester City da Tottenham
- Crystal Palace da Brighton
- Bournemouth da Newcastle United
Sai a ranar Lahadi za a yi wasa biyu tsakanin Leeds United da Manchester United da na Manchester City da Aston Villa.
A ranar Laraba United ta tashi 2-2 da Leeds United a Old Trafford, wadda ta kori kociyanta Jesse Marsch a kwantan karawar mako na takwas a Premier.
Za a yi wasan hamayya na Mersyside Derby tsakanin Liverpool da Everton ranar Litinin a Anfield.
Liverpool tana ta 10 a teburin Premier da maki 29, ita kuwa Everton tana ta 18 da maki 18 ta ukun karshe kenan.