Za A Fara Samar  Da Motoci Masu Amfani Da Lantarki A Najeriya Daga  2018


Wani kamfani mallakar yan Najeriya mai suna Nigus Enfinity yace zai fara samar da motoci masu amfani da lantarki a kasuwar motoci ta Najeriya.

Malik Ado-Ibrahim, Shugaban kamfanin ya bayyana haka ga manema labarai a wani taron tattaunawa da yan jarida da ya gudanar a Abuja jiya Alhamis.

Ado-Ibrahim yace kasashen duniya da dama sun saka lokaci na daina amfani da motoci masu aiki da man fetur yayin da kasar India ta saka shekarar 2030 ita kuwa kasar Birtaniya zata daina amfani da motocin a shekarar 2040.

Yace Najeriya da kasashen Afirika ya kamata su zamo kan gaba wajen shiga juyin juya halin dake faruwar a bangaren kera motoci ko kuma su zama wata matartarar jibge motocin da aka daina amfani dasu a wasu kasashen. 

 Ado-Ibrahim wanda shine mutum na farko dan Afirika da ya jagoranci gasar tseren motoci ta duniya na Formula One a shekarar 1999 yace tuni kamfaninsa ya fara gina tashar samar da hasken wutar lantarki mai amfani da hasken rana da zata samar da 100mw a jihar Katsina da kuma Adamawa. 

 A cewar sa kamfaninsa ya na hada gwiwa da wani kamfanin kasar China dan shigo da motoci masu amfani da wutar lantarki cikin farashi mai sauki. 


Like it? Share with your friends!

0

You may also like