Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa NDLEA dake jihar Anambra ta gargadi yan siyasa dake jihar kan amfani da matasa a matsayin yan bangaran a zaɓen gwamnan jihar da za’a yi.
Kwamandan hukumar a jihar Sule Momodu shine yayi wannan gargadi yayin wani shirin rediyo na kai tsaye, ya kuma yin gargadi akan masu jan hankalin matasa wajen ta’ammali da miyagun kwayoyi.
Momodu ya dage kan cewa hukumar baza ta rashawa kowanne dan siyasa ba da aka samu da laifin yin amfani da kwayoyi ba bisa ka’ida ta hanyar ingiza matasa suyi amfani da kwayoyin.
Ya bayyana cewa a shirye hukumar ta NDLEA take ta hada kai da sauran hukumomin tsaro dan tabbatar da cewa an gudanar da zaɓen gwamnan jihar lafiya.