Za a je zagaye na biyu a zaben Turkiyya | Labarai | DWZa a je zagaye na biyu a zaben shugaban kasa da aka gudanar a Turkiyya ganin cewa Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya rasa samun rinjayen da ake tunani duk da cewa ya kasance a kan gaba.

Shugaba Erdogan dai na da kashi 49.4% na kuri’un da aka kada, abin da ya hana shi samun rinjaye a zaben na ranar Lahadin da ta gabata.

Babban abokin hamayyarsa a zaben Kemal Kiliçdaroglu kuwa ya tashi ne da kashi 44.7, kamar yadda hukumomin kasar ta Turkiyya suka nunar.

Dama dai babbar jam’iyyar adawa ta CHP ta zargi jam’iyya mai mulki ta Shugaba Erdogan wato AKP, da yin watsi da kuri’un da suka samu a yankunan da suke da karfi.

Jagoran na adawa ya ce, an dakatar da kirken kuri’u alal misali a Ankara da gangan, duk da cewa ana ci gaba da lasafta su a sauran yankuna, yayin da ita kuwa jam’iyya mai mulkin ta AKP ke zargin adawar da yi wa zaben kafar angulu.
 

Source link


Like it? Share with your friends!

1

You may also like