Za A Kammala Aikin Gina Layin Dogo Na Lagos Zuwa Ibadan A Watan Disambar 2018Ministan sufuri Rotimi Amaechi yace za’a fara amfanin da sabon layin dogo da ake ginawa tsakanin Lagos zuwa Ibadan cikin watan Disambar 2018.

   Ya bayyana haka lokacin da yake duba aikin tare da gwamnan jihar Ogun Ibikunle Amosun,  a Ijoko dake karamar Hukumar Ado -odo/Ota ta jihar Ogun. 

Yace tuni aka ware kudin gudanar da aikin  kuma gwamnatin tarayya ta bada himma wajen ganin an kammala aikin a watanni hudun karshen shekarar 2018.

“Munce 2018, wannan umarnin shugaban kasa ne, a watan Disamba muna so muga jiragen kasa na zirga-zirga tsakanin Lagos da Ibadan.”yace. 

“Mun mai da hankali wajen cimma wannan buri, tuni kudin da aka karba ciwo bashi daga Bankin kasar China suka iso domin ganin cewa babu wani abu da yakawo tsaiko.”

Amma Amaechi yayi nuni da cewa ya zuwa yanzu aiki ya dakata saboda tsayin wasu gadojin sama guda biyu a jihar. 

 ” Cikas na farko da dan kwangilar ya gano shine wasu gadojin mutane na tsallaka titi guda biyu a jihar Lagos (a Oshodi da Ikeja) sai kuma gadar sama da ake ginawa a Ijoko. ”

Amaechi yace injiniyoyi baza su cigaba da aiki ba har sai an shawo kan wadannan matsalololi. 

You may also like