Za a kammala aikin gina tashar jirgin ruwan Baro a wannan shekara


Sakataren gwamnatin tarayya, Mista Boss Mustafa,  yace za a kammala aikin gina tashar jirgin ruwan Baro dake jihar Neja a shekarar 2018.

Wata sanarwa da tafito daga ofishinsa tace sakataren ya bayyana haka ne lokacin da ya karbi bakuncin gwamnan jihar Neja Abubakar Sani Bello a ofishinsa dake Abuja.

Sanarwar mai ɗauke da sahannun mataimakin daraktan yaɗa labarai a ofishin, Muhammad Nkorji tace sakataren ya tabbatarwa da gwamnan cewa aikin gina tashar na samun kulawar gaggawa daga gwamnatin tarayya.

“Aikin gina tashar jiragen ruwa dake  Baro na samun kulawar gaggawa daga gwamnatin tarayya na ganin cewa an kammala tare da kaddamar da fara amfani da tashar a wannan shekara.

Tun farko gwamnan yace  ya kai ziyarar ne domin taya sabon sakataren murna sannan ya kuma yaba da ƙoƙarin gwamnatin tarayya kan ƙoƙarin da take na kammala aikin gina tashar jirgin ruwa ta Baro.

You may also like