Za A Karrama Uwargidan Shugaban Kasa Tare Da Sarkin Kano…


Za A Karrama Uwargidan Shugaban Kasa Tare Da Sarkin Kano A Amurka.

Uwargidan Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha Buhari tare da wasu gwamnonin Nijeriya, manyan ‘yan kasuwa da kuma sarakuna da suka hada da Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, za su halarci wani taro, na bikin murnar shekaru 25 da kafuwar Kungiyar Zumunta a Kasar Amurka, wacce ta kunshi ‘yan Nijeriya ma zauna kasar dake wakiltar jihohin 19 na arewacin Nijeriya.

Babban Editan Sashen Hausa na Muryar Amurka, kuma shugaban tsare-tsare na gudanar da taron, na Kungiyar Zumunta mazauna Amurka, Alhaji Aliyu Mustapha Sokoto ne ya bayyana haka ga manema labarai a farkon wannan makon.

Taron wanda za a gudanar da shi ranar Asabar, shida ga Watan Agusta na wannan shekara birnin Washington, wanda suka kira bikin rubu’in Karni, zai tabo batutuwan da suka shafi muhimmancin amfani da kayayyaki ko kuma sanfurin cikin gida Nijeriya. Wadda a yanzu haka ma Jihohin Neja da Bauchi sun shirya tsaf, don baje kolin sanfurin kayan da aka kera a jihohinsu a yayin gudanar da taron.

Haka kuma taron zai duba batun naukar nauyin karatu kyauta, wadda kungiyar ta baiwa dubban dalibai daga sassa Arewacin Nijeriya a cikin fiye da shekaru 20 da suka gabata a kuma Jami’o’i da Kwalejojin ilmi daban-daban a Nijeriya. Inda kuma wasu daga cikin daliban da suka ci gajiyar tallafin za su bayyana irin nasarori da kuma matakan cigaban rayuwa da suka sakamakon tallafin.

Sannan Uwargidan Shugaban Kasar, Hajiya Aisha Buhari ita ce Babbar Bakuwa, yayin da Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II zai kasance babban bako mai jawabi a taron, mai taken “Gudumawar Da Mazauna Kasashen Waje Za Su Iya Bayarwa Wajen Gina Kasa”, wato (Collaboratibe Strategies with Nigerians in the Diaspora).

Hakazalika Gwamnonin Bauchi, Adamawa, Neja da kuma Kano za su halarci taron, yayin da ake tsammanin halartar Gwamnonin Sokoto, Borno da Yobe, kana kuma hamshakan Attajirai da suka hada Alhaji Aliko Dangote, Alhaji Muhammad Indimi da kuma T.Y Danjuma za su karawa taron armashi da halartar su.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like