Za A  Kashe Wani Mutum Ta Hanyar Rataya,Saboda Kisan Mahaifinsa Da Yayi A Kan Rabon GadoWata Babbar kotu dake babban birnin jihar Ekiti, Ado Ekiti, ta yankewa wani matashi mai suna Blessing Olumakinde Egunlae, hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan da ta same shi da laifin kisan mahaifinsa. 

Babban alkalin jihar mai Shari’a Ayodeji Daramola,wanda ya zartar da hukuncin  a jiya talata,yace hujjojin da suke gaban kotu sun tabbatar da cewa ,mutumin da ake zargi ya aikata kisan kai. 

Yace masu gabatar da kara sun tabbatar da kwararan hujjojin dake nuni da cewa mutumin lallai ya aikata laifin, saboda haka na yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

An dai gurfanar da Olumakinde,  ne bisa tuhumar kisan mahaifinsa mai mata 6 da kuma yaya 18.

Iyalin marigayin sun dade suna samun sabani kan rabon gonar da marigayi Egunlae  ya mallaka. 

Bayan da bai gamsu da yadda mahaifin  nasa yayi rabon ba, Olumakinde dan shekara 47, yabi sahun mahaifinsa zuwa gona, inda ya sassara shi da adda. 

Wata shida akayi ana nemansa kafin daga bisani ya mika kansa wurin yan sanda.

A bayanan da yayi wa yan sanda mutumin da ake zargi yace ya kashe mahaifinsa ne a cikin wani dakin Bukka dake cikin gonar. 


Like it? Share with your friends!

0

You may also like