Gimbiya Mako, ‘yar gidan sarautar Japan, za ta rasa darajarta bayan da ta amince da auren talaka. Gimbiyar mai shekara 25, wacce jika ce ga Sarki Akihito, za a yi mata baiko da Kei Komuro, wanda karamin ma’aikacin wani kamfani ne, bayan da suka hadu a jami’a.
Dokar sarautar Japan dai, ta bukaci gimbiya ta bar cikin iyalan gidan sarki da zarar ta auri talaka.