
Asalin hoton, Google
Hukumar kula da muhalli ta Uganda ta ce za ta fara sanya tara ga direbobi daga watan Afrilu mai zuwa, ga duk wanda aka kama babu kwandon shara a motarsa.
Duk wanda aka kama za a ci tararsa kuɗin ƙasar shilling miliyan shida, kwatankwacin dalar Amurka $1,630, kamar yadda dokar da aka sanar ranar Laraba ta yi bayani.
Direbobin da suka ƙi biyan tarar za a gabatar da su gaban kotu ko kuma a tura su gidan yari, kuma kotu ce za ta faɗi yawan tarar, kamar yadda hukumar ta bayyana a sanarwarta.
A yanzu wajibi ne ga duk wata mota da ke ɗaukar fasinjoji su yi doguwar tafiya, ta sanya kwandon zuba shara a cikinta.
Amma faɗaɗa dokar da aka yi kan masu amfani da motocinsu na kansu ya janyo hayaniya a Uganda, yayin da wasu da yawa ke tambaya kan wane irin kwando za a yi amfani da shi.
“Matuƙar kana amfani da abin da ba zai iya riƙe dattin da ka ke amfani da shi ba a mota, to lallai za a ci tararka. Ba a yarda a yi amfani da ledoji ba a motar,” in ji kakakin hukumar Naomi Karekaho.
Ta ce hukumar za ta bayyana me take nufi da abin zuba sharar idan za ta faɗi sauye-sauyenta a nan gaba.
“A duka dokokin da muka bayyana na kiyaye muhammli wannanta fi tsaya wa mutane a rai. Wataƙila saboda an ce mutane su sa kwandon shara a mota,” ya ƙara da cewa.