
Asalin hoton, Hansons Auctioneers
Za a yi gwanjon rigar kwallon da aka dinka domin tsohon dan kwallon Brazil Pele kafin ya yi ritaya daga ƙwallo.
An kiyasta cewa rigar za ta kai kusan fam dubu 30.
Kamfanin gwanjon kaya, Hansons ya ce rigar mai lamba 10, an yi wa Pele ne domin wasan Brazil da Yugoslavia a shekarar 1971.
Sai dai Pele bai saka rigar a lokacin wasan ba, amma sai ya bai wa wani dan kallo.
Daga bisani wani mai shagon abinci ne ya sayi rigar kafin wani matashi dan shekaru 33 ya saye ta a shekara ta 2020.
“Rigar na bukatar a ci kasuwa da ita,” in ji mutumin da zai sayar da rigar.
Pele ya mutu a watan Disambar bara kuma shi ne kadai dan kwallon da ya lashe gasar cin kofin duniya sau uku.
Hukumar kwallon duniya, Fifa ta karrama shi a matsayin gwarzon dan kwallon wannan karnin a shekara ta 2000.
Pele ya ci kwallo 1,281 a wasa 1,363 cikin shekaru 21 da yayi yana murza leda.
A ranar 15 ga watan Fabarairu za a yi gwanjon rigar.