
Asalin hoton, Getty Images
Za a yi gwanjon rigar Pele mai lamba 10 ta tawagar Brazil ta karshen wasansa a tamaula kan fam 30,000.
Daya ce daga riga biyu mai lamba 10 da aka yi a wasan Brazil da Yugoslavia a 1971 in ji kamfanin gwanjon, Hansons.
Koda yake Pele bai sa rigar ba a wasan, amma ya bayar da ita kyauta ga Abilio Jose de Silva da ake kira Nocaute Jack, wanda ya yi aiki da tawagar Brazil tsakanin 1960 zuwa 1994.
Asalin hoton, Hansons Auctineers
Daga baya ne wani mai gidan abinci a Shropshire ya sayi rigar, wanda ya yi fatan za a ajiye ta a dakin adana kayan tarihi.
Mai shekara 33, wanda baya son a bayyana sunansa ya ce ya sayi rigar a 2020 daga wani mai tara tsoffin abubuwan tarihi a fannin tamaulla.
Za a sayar da rigar ranar 15 ga watan Fabrairu.
Pele ya ci kwallo 1,281 a wasa1,363 a shekara 21 da ya yi yana taka leda, har da 77 da ya ci wa Brazil a karawa 92.
Pele ya mutu a Disambar 2022. Shi ne dan wasa tilo da ya lashe kofin duniya karo uku, an karrama shi da kyautar fitatcen dan kwallon duniya a karni da aka yi masa a 2000.