
Asalin hoton, Getty Images
Za a yi gwanjon rigunan wasa shida daga cikin rigunan da Lionel Messi ya saka a lokacin wasannin Argentina a gasar Kofin Duniya ta 2022 da aka yi a Qatar
Kyaftin Messi, mai shekara 36, ya ɗaga kofin ne bayan da suka doke Faransa a a wasan karshe na gasar.
Rigarsa ta wasan ƙarshe na kunshe cikin jerin rigunan da ake sa ran za su samu sama da fam miliyan takwas a gwanjon da Sotheby ta shirya a birnin New York.
Rigar ƙwallon ƙafa wanda ta fi daraja ita ce ta Diego Maradona da ya sanya a gasar Kofin Duniya ta 1986, wacce aka sayar kan fam miliyan 7.1 a shekarar 2022.
Brahm Wachter, shugaban masu tara kayayyaki na zamani na Sotheby, ya ce sayar da riguna shida na Messi “ya zama babban abin alfahari a tarihin gwanjon kaya”.
Messi, wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or sau takwas, ya zama ɗan wasa na farko a tarihin gasar Kofin Duniya da ya ci kwallo a kowanne mataki a gasar, tun daga rukuni har zuwa wasan ƙarshe.