Za a fara nuna shirin fim da aka yi kan rayuwar Ma’aiki SAW


 

A ranar 28 ga watan Oktoban nan za a fara nuna shirin fim din “Annabi Muhammad: Jakadan Allah” wanda ke dauke da tarihin Ma’aikin, rayuwarsa da kuma zuwan Annabtarsa.

Daraktan shirya fina-finai na kasar Iran Majid Majid ne ya rubuta shirin fim din tare da bayar da umarni inda tuni aka fara nuna wani bangare na shirin a gidajen cinema na Turkiyya.

A cikin shirin fim din an yi amfani da wani salo da tunani na daban don bayar da labarain rayuwar Annabi Muhammad Sallalahu Alaihi Wa Sallam tun daga haihuwa har zuwa shekaru 12 da kuma abubuwanda suka faru a Makka a wannan lokaci.

A shekarar 2015 aka kammala shirya fim din wanda ake sa ran zai kara haskaka duniya game da Risala.

Jarumai irin su: Sareh Bayat, Mohsen Tanabandeh, Rana Azadivar, Ali Reza Shoja-nuri da Mina Sadat na cikin wadanda suka taka rawa a cikin shirin fim din.


Like it? Share with your friends!

-1

You may also like