Za a kaddamar da farmaki na karshe akan Boko Haram


 

 

Kasashen da ke kewaye da tafkin Chadi da ke fada da Boko Haram, za su kaddamar da sabon farmaki akan ‘yan kungiyar bayan kawo karshen taron manyan hafsoshin kasashen a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar.

Kasashen na shirin kai wani gagarumin farmaki ne na karshe kan ‘yan Boko Haram a yankin.

Taron wanda ya hada manyan hafsoshin soji daga kasashen Najeriya da Nijar da Chadi da Kamaru da Jamhuriyar Benin, wata dama ce domin tsara yadda za a kaddamar da farmaki na karshe da nufi kawo karshen ayyukan kungiyar Boko Haram baki daya a yankin.

Ministan tsaron Jamhuriyar Nijar Hassoumi Massaoudou, ya ce rundunar hadin-gwiwa ta kasashe, ta samu gagarumar nasara a cikin watannin da suka gabata, tare da kwato gagaruwa da suka jima karkashin ikon kungiyarBoko Haram, tare da killace kungiyar domin hana ta samun kayan aiki.

A cikin watanni da suka gabata, kawancen dakarun kasashen na tafkin Chadi da Benin ya yi nasarar fatattakar dakarun kungiyar Boko Haram daga garuruwan Damasak da Abadan da kuma Gashagar, da ke cikin jihar Borno tare da bai wa jama’a damar sake komawa domin ci gaba da rayuwa a garuruwansu.

Taron da manyan hafsoshin suka gudanar a jiya alhamis a birnin Yamai, shi ne zai shata dubarun karshe kan yadda za a murkushe kungiyar ta Boko Haram baki daya.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like