Jam’iyyar masu ra’ayin rikau a Austriya tare da jam’iyyar masu kyamar baki sun gabatar da yarjejeniyar da suka cimma ta kafa gwamnati ga shugaban kasar Alexander Van der Bellen.
Sebastian Kurz ministan harkokin waje wanda jam’iyyarsa ta ÖVP ta samu nasara a zaben ‘yan majalisun dokoki a watan Oktoba. Ya bude shawarwari da jam’iyyar masu kyamar baki ta FPÖ ta Heinz Christian Strache don samun rinjaye don kafa gwamnati. A shekara ta 2000 kungiyar tarrayar Turai ta sakawa Austriya takunkumin karya tattalin arziki bayan da jam’iyyar masu kyamar bakin ta shiga gwamnati.