Mataimakin shugaban kasar Nijeriya farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta dauki ma’aikata guda 200,000 a karshen watan nan na Oktober.
Yayin da ya ke magana da manema labarai a fadar shugaban kasa Buhari, Osinbajo ya kara da cewa yanzu haka an yi nisa a shirye shiryen da ake na tabbatar da cewa mutane sun karu da sabon shirin ta na inganta rayuwar al’umma.
Manufar bayarda ayyukan shi ne domin a hana matasa zaman banza, sannan a biya su dan wani abu da za su kula da kansa, sannan su samu gogewa.
Wadannan ayyuka na daga cikin ayyukan da za’a baiwa mutane 500,000 a karkashin shirin N-Power na gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Mataimakin shugaban kasa ya bayyana kudirin su na kara daukar wasu kafin karshen shekarar nan.