Gwamnatin Neja ta sha alwashin cigaba daga turban da tsohuwar gwamnatin Injiniya Abdullahi Abdukadir Kure ta faro, domin a cewarta, gwamnatinsa ta fuskanci alkiblar samar da walwala da jin dadin jama’ar jihar ne.
Gwamnan Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello ya bayyana hakan a lokacin da yake karban bakunci masu zuwa ta’aziyyar tsohon gwamnan wanda ya rasu a makon jiya.
Gwamna Abubakar Sani Bello ya ce Gwamnatin Kure ta himmantu wajen samar da hanyoyi a yankunan karkara da birane gami da inganta ruwan sha ga jama’a tare da samar da gurabun aiki, a cewar shi wannan turba ce abin koyi, “lallai wannan gwamnatin za ta himmantu a inda ya tsaya domin samar da kyakkyawar jiha mai albarka”.
Gwamnan ya cigaba da cewar gwamnatinsa da majalisar dokokin jiha za ta kafa wani abin tarihi wanda zai sa a rika tunawa da kyawawan halayen marigayin, wanda shi ne gwamna na 12, a tsarin gwamnonin da suka mulki jihar. “Lallai duk ayyukan da ya somo bai kammala ba za mu tabbatar mun kammala su wanda abin alfahari ne a wajenmu”.
Gwamnan ya kuma ce rashin mutum irin A. A Kure babban rashi ne a jiha da kasa, saboda zamowarsa dattijo mai tunani da hangen nesa a kan son cigaban kasar nan wanda ke da kyakkyawan dabarun siyasa mai amfani ga jama’a.
Daga cikin wadanda suka ziyarci Gwamnan dan jajantawa akwai tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, shugaban rundunar ‘yan sanda ta kasa, IG Ibrahim Idris, sai Gwamnonin Adamawa, Bindo Jibrilla, Ibrahim Dankwanbo na Gombe, Abdullahi Umar Ganduje na Kano da Aminu Waziri Tambuwal na Sokoto.
Sauran sun hada da shugaban Majalisar Dattijai, Bukola Saraki, da Sanata Bala Ibn Na’alla, da Hon. Ado Duguwa wanda shi ya wakilci shugaban Majalisar Wakilai ta Kasa, Hon. Yakubu Dogara.