
Asalin hoton, OTHER
Kocin Arsenal Mikel Arteta ya ce za su shiga kasuwa a watan Janairu, biyo bayan raunin dan wasan gabansu Gabriel Jesus.
Jesus ya ci wa Gunners kwallaye biyar ya kuma taimaka aka ci shida a kakar bana a gasar Premier League kafin aje hutun Qatar 2022.
Sai dai mai shekaru 25 din ya samu rauni a lokacin da yake wakiltar kasarsa a gasar kofin duniya da aka kammala a Qatar.
Tuni an yi wa Jesus aiki, kuma zai shafe lokaci kafin ya dawo fagen daga.
”An yi masa aiki, kuma hakan ya isa yasa a fahimci munin raunin da ya samu. Saboda haka za mu shiga kasuwa mu darje daga ‘yan wasan da kenan,” in ji Arteta.
Ya kara da cewa ”rashin Jesus saboda raunin da ya samu babban cikas ne.”
Mikel Arteta ya kuma ce abu ne mai wahala ya iya fadin sadda Jesus zai murmure, la’akari da munin raunin da ya samu.
A ranar 26 ne Arsenal za ta karbi bakuncin West Ham a filin Emirates, a wasa na farko bayan dawowa hutun gasar cin kofin duniya.