‘Za mu rufe bankuna domin kare rayuwar ma’aikatanmu’Economy
Bayanan hoto,

‘Yan Najeriya na kwana a kan layukan neman kudi a banki

Kungiyar ma’aikatan Bankuna da Insora ta Najeriya ta yi barazanar janye ‘yan kungiyar a daukacin fadin kasar sakamakon hare-hare da ake kai wa harabar wasu bankunan kasuwanci a kasar.

Hakan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da fuskantar karancin Naira wani abu da ke fusata masu hulda da bankunan.

Sakataren kungiyar na kasar Mohamamd Sheikh ya shaida wa BBC cewa ” sakamakon fusatar da mutane suke yi sai su rinka kai wa ma’aikatanmu hari da duka da zagi da duk nau’in cin mutumci,

muna tsoron ka da al’amarin ya wuce gona da iri da ka iya kai wa ga kisan kai ko wani abu makamancin hakan.”Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like