
Asalin hoton, DIKKO RADDA/FACEBOOK
A Najeriya, zababben gwamnan jihar Katsina Dikko Umaru Radda karkashin jam’iyyar APC mai mulki, ya ce gwamnatinsa za tayi aiki da kowanne bangare na al’umma domin tabbatar da ta ciyar da jiharsa gaba.
Radda ya ce abun da zai maida hankali akai shi ne ciyar da Katsina gaba da kawo sauyte say
Dikko Umaru Radda ya kuma ce ya yi mamaki wasu zarge-zarge da batutuwan da suka biyo bayan zaben da ya bashi nasara, sai dai kuma ba shi da wata fargaba domin ya san al’umma jihar Katsina ne suka zabe shi, saboda gamsuwa da manufofinsa.
Kan batun ‘yan adawa musamman jam’iyyar PDP da Sanata Yakubu Lado Danmarke ya yi zargin an tafka magudi da aringizon kuri’u a lokacin zaben gwamnan da aka yi ranar 18 ga watan Mayu, da shan alwashin daukar matakin shari’a, Dikko Radda ya ce ba ya ko dar domin ya san an yi sahihin zabe a jihar Katsina.
”Wato duk wani dan siyasa bai cika faduwa zabe, ya mika lamari da kallon hakan a matsayin kaddara ce ta sanya hakan faruwa ba, amma idan aka kalli yanayin zaben an san jama’a a jihar Katsina sun waye sun kara banbance aya da tsakuwa.
Sannan zaben gwamna shi aka fi fitowa fiye da zaben shugaban kasa. zargin da ‘yan adawa suke yi na magudin zabe ba za a hana su ba, amma ina son shaida muku mutanen jihar Katsina sun zabi cancanta.
Abin mamakin shi ne dukkan runfunan zabe da mazabu ne aka yi magudin, duk wani wuri da ake zuwa kamfe har da yankunan da ake fama da matsalar tsaro, mun shiga, mazabu 360 a jihar Katsina na je, mutanen jihar Katsina cancanta suka zaba.”
Radda ya ce a shirye ya ke ya yi aiki da kowa da kowa, domin gudanar da ayyukan ci gaba a jihar Katsina, ba tare da la’akkari bangare ko jam’iyyar da ya fito ba.
”Babban abin da zan mai da hankali akai shi ne maganace matsalar tsaro da jiharmu ke fama da shi, da kuma bunkasarta da ayyukan ci gaba.
Ina kira ga kowa da kowa, da wadanda muka tsaya takara tare da ‘yan adawa da sauran mutane, su zo mu yi aiki tare domin duk wanda ya tsaya takarar gwamna a jihar Katsina abin da ke gabansa shi ne samawa jihar ci gaba ta fannoni da dama.
Za mu karbi shawarwarinsu da dabarunsu, mu hada da namu domin yin aikin da zai bunkasa al’umarmu. Fatan mu shi ne mu cika alkawarin cika alkawarin da muka daukarwa al’umar jihar Katsina”
Fafatawa a zaben na jihar Katsina ta fi karfi tsakanin Dikko Umaru Radda na jam’iyyar APC mai mulki, da Sanata Yakubu Lado Danmarke na babbar jam’iyyar adawa ta PDP, da ya kalubalanci nasarar da Radda ya samu tare da alwashin kalubalantarsa a gaban shari’a.